Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Yarjejeniyar tsaro tsakanin Moscow da Bangui

Dakarun wanzar da zaman lafiya da tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Bangui
Dakarun wanzar da zaman lafiya da tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Bangui MARCO LONGARI / AFP

Rasha ta kulla yarjejeniyar tsaro da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kasa da wata daya bayan da wasu ‘yan bindiga suka hallaka ‘yan jaridar kasar ta Rasha uku da ke bincike dangane da ayyukan sojin hayar kasar ta Rasha a wannan kasa da ke fama da rikici.

Talla

Ministan tsaron Rasha Seigei Shoiyu da takwaransa na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Mairie-Noelle Koyara ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a birnin Moscow.

Daga bisani mataimakin ministan tsaron na Rasha Alexander Fomin ya shaida wa manema labarai cewa, ko baya ga batun tsaro, yarjejeniyar ta kuma kunshi wasu batutuwa ciki har da ilimi a tsakanin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.