Faransa-Mali

Sojin Faransa sun kashe jagoran 'yan ta'adda a Mali

Sojin Faransa sun kwashe tsawon shekaru suna aikin yakar 'yan ta'adda a Mali
Sojin Faransa sun kwashe tsawon shekaru suna aikin yakar 'yan ta'adda a Mali REUTERS/Joe Penney

Rundunar sojin Faransa ta ce, wani harin sama da dakarunta da ke yaki da yan ta’adda ta kai a Mali, ya yi sanadiyar mutuwar wani babban jagoran kungiyar ‘yan ta’addan ta ISGS.

Talla

Sanarwar da rundunar ta bayar a birnin Paris, ta ce bayan kaddamar da harin a yankin Menaka, dakarun sojin sun tabbatar da kashe Mohammed Ag Almouner da mai tsaron lafiyarsa, yayin da suka gano gawar wata mata da yaro a kusa da wurin da aka kai farmakin.

Sanarwar ta bayyana takaici kan mutuwar fararen hular biyu duk da cewa, ba a tabbatar da alakar da ke tsakaninsu da mayakan ba.

Kungiyar ISGS wadda ke karahsin shugabancin Adnan Abu Walid Sahrawi, na da tunga a kan iyakar Mali da Burkina Faso kuma ta kan kai hari a Nijar, yayin da sojojin Faransa suka kwashe tsawon shekaru suna yakar su da zummar maido da zamana lafiya a yankin.

ISGS ta dauki alhakin farmakin da ya hallaka sojojin Nijar hudu da na Amurka hudu a cikin watan Oktoban shekarar 2017 a Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI