Najeriya-Zabe

APC ta nemi jihohi su zabi tsarin fitar da ''yan takarar da suke so

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban Jam'iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomole.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban Jam'iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomole. Duisaf.com

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta bai wa 'ya'yan ta damar bayyana irin zaben fidda gwanin da su ke bukata a musu dangane da shirin zaben shekara mai zuwa.

Talla

Jam’iyyar ta kuma amince da gudanar da zaben Yar tinke wajen tsayar da dan takaran shugaban kasa kamar yadda shugaba Muhamamdu Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo suka bukata.

Matakin wanda aka cimma yayin wani taron shugabannin Jam'iyyar karon farko bayan gagarumin gibin da ta fuskanta na ficewar wasu jiga-jiganta ana ganin shugaban kasar ba zai fuskanci wata tabgarda ba, la'akari da yadda baya da wani abokin karawa a cikin jam'iyyar.

Matakin na APC na zuwa a dai dai lokacin da shugaban Majalisar Dattijan kasar Bukola Saraki ya bayyana ra'ayinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben na 2019.

A bangare guda shi ma Sanatan Kano ta tsakiya Rabi'u Musa Kwankwaso ya sha alwashin kayar da shugaban Najeriyar a zaben na 2019 ko da dai ana ganin zai gamu da cikas la'akari da yadda masu son takarar shugabancin kasar a Jam'iyyar PDP ke da tarin yawa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI