Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta hallaka sojin Najeriya 30 a Borno

Rahotanni daga Najeriya na cewa akalla dakarun Sojin kasar 30 ne suka hallaka yayin wata fafatawarsu da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabas da ke gab da kan iyakar kasar da Jamhuriyyar Nijar.

Wata tawagar Dakarun sojin Najeriya kenan da ke aikin yaki da ta'addanci a Jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram.
Wata tawagar Dakarun sojin Najeriya kenan da ke aikin yaki da ta'addanci a Jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram. CNBC Africa
Talla

Wasu majiyoyin Tsaro sun tabbatar da mutuwar dakarun kusan 30 tare da raunata da dama bayan wani farmaki da mayakan na Boko Haram suka kai sansaninsu.

A cewar Majiyoyin tun a ranar Alhamis ne wani adadi mai yawa na Mayakan Boko Haram din ya dirar sansanin Sojin Najeriyar da ke kauyen Zari a arewacin jihar Borno gab da kan iyaka, kuma bayan daukar tsawon lokaci ana fafatawa mayakan suka yi nasara fatattakar dakarun sojin tare da hallaka kusan 30.

A baya-bayan nan dai ana yawan samun kai farmaki kan dakarun sojin wanda a lokuta da dama akan hallakasu tare da tarwatsa wasu zuwa dazuka, inda ko a kwanakin baya an samu tarin dakarun sojin da suka bace a daji ko da dai shalkwatar rundunar sojin Najeriyar ta ce ba haka abin ya ke ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI