Senegal

Shugaba Macky Sall ya dakatar da Khalifa Sall

Karim Wade et Khalifa Sall ,Yan takara biyu da kotun ta dakushe bukatar kalubalantar shugaba Macky Sall a zabe
Karim Wade et Khalifa Sall ,Yan takara biyu da kotun ta dakushe bukatar kalubalantar shugaba Macky Sall a zabe Montage: RFI / AFP Photo/Stringer (g) / CC-BY-SA Skolkovo (d)

A Senegal bayan da kotun Koli ta dakushe bukatar biyu daga cikin yan takarar shugabancin kasar Khalifa Sall da Karim Wade na kalubalantar shugaba Macky Sall a zaben shugaban kasa,Macky Sall Shugaban kasar ya sanya hannu a wata ayar doka dake dakatar da Khalifa Sall daga mukamin magajin garin Birnin Dakar .

Talla

Yan adawar guda biyu na da tarin magoya bayan da ake ganin zasu iya yiwa shugaba Sall barazana, yayin da lauyoyin su ke cewa gwamnati na amfani da kotunan ne wajen hana su tsayawa zaben.

A shekarar 2015 aka daure Karim Wade shekaru 6 a gidan yari saboda samun sa da laifin azurta kan sa da kudaden gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.