Uganda

Yan Sanda sun sake tsare Bobi Wine

A Uganda,yan Sanda sun sake tsare mawwakin nan kuma dan Majalisa Robert Kyagulanyl da aka yiwa lakabi na Bobi Wine a dai dai lokacin da yake shirin barin kasar zuwa Amurka domin samun kulawa.

Dan Majalisar kasar Uganda  Bobi Wine
Dan Majalisar kasar Uganda Bobi Wine Isaac Kasamani/AFP
Talla

A cewar lauyan sa, yan Sanda sun azbatar da shi a lokacin da yake tsare, zai yi tafiya ne domin samun kulawa daga likitoci a Amurka.

Kakkakin yan Sanda a Kampala ya bayyana cewa sun sake tsare dan Majalisar ne domin gudanar da bincike don gano gaskiyar zargin da yake yi na cewa an ci zarrafin sa, wanda hakan ya kaucewa dokokin kasar ta Uganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI