Najeriya-Buhari

Bana fargabar gudanar da sahihin zabe a Najeriya - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martinin kan kiraye-kirayen da ake masa wajen ganin ya gudanar da sahihin zabe karkashin shugabancinsa a shekarar 2019.

Talla

Muhammadu Buhari wanda yanzu haka ke can a birnin Beijing na kasar China ya ce ko kadan baya tsoron a gudanar da zaben na 2019 kan doron gaskiya ba tare da magudi ta kowacce fuska ba, domin kuwa shi kansa ya amfana da sahihin zabe a 2015.

Da ya ke zantawa da al’ummar Najeriya mazauna China, Muhammadu Buhari ya ce zai yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ‘yan najeriya sun samu abin da suka zaba a babban zaben na badi.

Mabanbantan bangarori kama daga na cikin kasar da kuma na ketare ne ke ci gaba da kir aga shugaban na Najeriya wajen ganin ya yi tsayuwar daka don gudanar da zabe mai inganci a dai dai lokacin da ya rage watanni bakwai al’ummar kasar su kada kuei’unsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.