Afrika ta Kudu

Fararen fata za su tsunduma yajin aiki a Afrika ta kudu

Shugabanci karkashin Cyril Ramaphosa a Afrika ta kudu na da nufin samar da daidaito tsakanin bakaken fata da farare wadanda ke rike da kaso mai yawa na arzikin kasar.
Shugabanci karkashin Cyril Ramaphosa a Afrika ta kudu na da nufin samar da daidaito tsakanin bakaken fata da farare wadanda ke rike da kaso mai yawa na arzikin kasar. Themba Hadebe / POOL / AFP

Dubban fararen fata ma’aikatan kamfanin ma’adinai na Sasol da ke Afrika ta kudu sun shirya tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a gobe litinin bayan wani shirin gwamnatin kasar na yin raba dai-dai tsakanin fararen fatar kamfanin da bakaken fata ta fuskar kadadrorin da suka mallaka.

Talla

Matakin wanda gwamnatin ta gabatar karkashin shirinta na bunkasa tattalin arzikin bakaken fata, ta nemi ilahirin kamfanonin kasar su cimma daidaito kan yadda za a yi raba dai dai na mamallakansu tsakanin bangaren fararen fata da bakake, wanda ke da nufin kawo karshen takaddamar dimbin shekaru da ke tsakaninsu.

Sanarwar da kungiyar kwadago bangaren fararen fata a kamfanin na Sasol ta fitar ta ce ma’aikatanta fiye da dubu 6 da dari 3 da ke kamfanin za su tsunduma yajin aikin a gobe Litinin.

Kamfanin Sasol wanda ya yi kaurin suna ta fannin kimiyyar mayar da gawayi da Iskar gas zuwa man fetur a bara ne yasha alwashin raba dai dai kan nau’in mutanen da suka mallaki sassanshi tsakanin fararen fata da bakake.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.