Chadi

Sojan saman Chadi sun kai farmaki kan yan tawaye a Tibesti

Idriss Déby, Shugaban kasar Chadi
Idriss Déby, Shugaban kasar Chadi Ludovic MARIN / AFP

Rundunar saman Chadi ta yi ruwan wuta saman yan tawaye a lardin Tibesti dake arewacin kasar daf da kan iyaka da kasar Lybia.Farmakin dake zuwa yan kwanuki bayan da gwamnatin Chadi ta bayar da umurnin rufe dukkanin wuraren hakar zinari da ke yankin arewacin kasar iyaka da Libya, biyo bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a garuruwan Miski da Kouri Bougri da ke yankin.

Talla

Wuraren da suka kasance maboya ga yan tawaye dake fada da sojan Chadi sun hada da Miski da Yebibou, wanda tun a watan Agustan da ya shude ne Gwamnatin kasar ta kaddamar da shirin kakkabe yan tawaye daga yankunan.

Yankin na Tibesti ya kasance wani yanki da masu hako zinari suka mamaye kama daga shekaru na 2012 zuwa 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.