Mali

Yan adawa na ci gaba da zanga-zanga a Mali

Magoya bayan dan Adawa Soumaila Cisse a Bamako
Magoya bayan dan Adawa Soumaila Cisse a Bamako ANNIE RISEMBERG / AFP

A Mali , yayinda da mutanen kasar ke cikin dakon rantsar da Shugaba Ibrahim Boubacr Keita ranar talata 4 ga watan Satumba, jam’iyyun adawa a karkashin jigon su Soumeila Cisse sun gudanar da zanga-zanga lumana a jiya a babban birnin kasar Bamako domin nuna rashin amincewar su da sakamakon zaben kasar.

Talla

Dan adawar Soumaila Cisse ya jaddada cewa za su ci gaba da neman hakin su, domin zaben da ya gudana a kasar na tattare da kuskure.

Magoya bayan Shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita za su gudanar da ta su zanga-zangar nuna goyan baya a yau lahadi a Bamako.

Sakamakon da hukumar zaben kasar ta Mali ya nuna cewa shugaba mai ci Ibrahim Boubacar Keita ya samu kashi 67 na kuri’un da aka kada, yayinda Souma’ila Cisse ya samu kashi 32.8 na kuri’un da aka kada a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu da ya gudana a ranar Lahadi 12 ga watan Agusta, 2018.

A zagayen farko na zaben da ya gudana a ranar 29 ga watan Yuli, Keita ne ya fi samun kuri’u da sama da kashi 41 cikin 100, yayinda Souma’ila Cisse ya samu kashi 17 cikin 100. Rashin samun dan takarar da ya lashe kuri’u kashi 50 a zagayen farko ne ya sabbaba kaiwa ga zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.