Turai-Nijar

Turai zata taimaka wajen yaki da safarar bakin haure a Nijar

Wasu bakin haure cikin dajin Sahara na Agadez
Wasu bakin haure cikin dajin Sahara na Agadez RFI/Bineta Diagne

Kungiyar kasashen Turai tace ta baiwa Jamhuriyar Nijar euro miliyan 21 domin taimaka mata wajen yaki da safarar bakin dake bi ta cikin kasar ta zuwa Turai.

Talla

Sanarwar da kungiyar ta bayar a yau, ta nuna cewar an zuba kudaden ne a Baitulmalin Nijar a farkon watan jiya, wanda ake saran amfani da su wajen inganta tsaron cikin gida da na kan iyaka da kuma yaki da safarar mutane.

Sanarwar tace wannan tallafin ya kawo adadin kudaden da aka baiwa kasar zuwa euro miliyan 51 a farkon shekarar 2018.

Kungiyar tace akwai wasu karin kudaden da zata baiwa kasar a watanni 3 na karshen wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.