Algeria

Algeriya ta nada sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa

Kungiyar kwallon kafar Algeriya ta  Fennecs
Kungiyar kwallon kafar Algeriya ta Fennecs REUTERS/Denis Balibouse

Hukumar kwallon kafar Algeriya ta sanar da nada sabon mai horar da kungiyar kasar tsohon dan wasan kulob na Marseille a Faransa Djamel Belmadi.Belmadi ya maye gurbin tsohon dan wasan kasar kuma mai horar Rabah Madjer.

Talla

Belmadi mai shekaru 42 da ya samu haskawa a kulob na Marseille na kasar Faransa kama daga shekara ta 2000 zuwa 2003 ya rataba hannu a kwantragi na shekaru hudu da kungiyar kwallon kafar ta Algeriya.

Nauyin dake wuyan sa shine na kai kungiyar ta Algeriya ga nasarar samun tikiti zuwa gasar cin kofin Afrika a shekara ta 2019 da kuma gasar cin kofin Duniya a Qatar a shekara ta 2022.

Tarihi ya nuna cewa Belmadi ya taba horar da kungiyar kwallon kafar Qatar tsawon shekara daya a 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.