Mali

An rantsar da Ibrahim Boubacar Keita a Bamako

An rantsar da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita domin yin wa’adi na biyu sakamakon nasarar da ya samu a zaben da ya gabata a Bamako.

Ibrahim Boubacar Keïta Shugaban Mali
Ibrahim Boubacar Keïta Shugaban Mali REUTERS/Annie Risemberg
Talla

Zababben shugaban ya sha alwashin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin kasar, a matsayin babban abinda zai sanya a gaba.

Sai dai yayin da ake gudanar da rantsuwar yan tawaye sun kai hari garin Menaka, inda suka raunana sojin Majalisar Dinkin Duniya dake aikin samar da zaman lafiya guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI