Najeriya

Ana ci gaba da samun karin yan takara a Najeriya

Akwatin zabe a Najeriya
Akwatin zabe a Najeriya

A Najeriya ana cigaba da samun karin masu bayyana aniyar su ta takarar shugabancin kasar a zaben shekara mai zuwa a Jam’iyyu daban daban.Jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta bai wa 'ya'yan ta damar bayyana irin zaben fidda gwanin da su ke bukata a musu dangane da shirin zaben shekara mai zuwa.

Talla

Bayan da yan takara irin su shugaban kasa Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar da Sule Lamido da Ahmed Makarfi da suka bayyana takarar su, na baya bayan nan sun hada da tsohon shugaban majalisar Dattawa David Mark da Tsohon Gwamna Donald Duke.

Mun tambayi Muhammad Hashim Suleiman na Jami’ar Ahmadu Bello ko yaya yake kallon yawan yan takaran, sai ya kada baki yace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.