Congo Dimokuradiyya

Bemba ya bayyana furucin sa

Jean-Pierre Bemba, Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo
Jean-Pierre Bemba, Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo JOHN THYS / AFP

Tsohon Shugaban yan Tawayen Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo Jean Pierre Bemba ya bayyana matsayin kotun kolin kasar na hana shi takarar zabe a matsayin kama karya.

Talla

A jamhuriyar demokradiyar Congo hukumar zaben kasar ta kori yan takara 6 daga cikin 25 dake bukatar tsaya wa a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a ranar 23 ga watan desembar wannan shekara 2018

‘Yan takarar da aka kora, sun hada da daya daga cikin manyan yan adawar shugaba Josèphe Kabila, cewa da Jean-Pierre Bemba, a kan laifin gabatar da shaidun karya a shara’arsa ta kotun duniya, da kuma tsohon fara ministan kasar Antoine Gizenga, da Adolphe Muzito da Sami Badibanga, sai Jean-Paul Moka-Ngolo da kuma uwargida Marie Josée Ifoku.

Bemba yayi zargin cewar gwamnatin kasar na katsalandan cikin shirin zaben wajen zaben dan takarar da suke so su fafata da shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.