Kamaru

An kai hari a wata makaranta dake yankin yan aware na Kamaru

Sojojin Kamaru a yankin yan aware
Sojojin Kamaru a yankin yan aware AFP

A Kamaru wasu dalibai 5 sun bata bayan wani hari da aka kai wata makaranta a yankin da ake amfani da turancin Ingilishi, inda aka raunana mutane da dama cikin su harda shugaban makarantar.

Talla

Shaidun gani da ido sun ce an kai harin ne makarantar sakandaren dake garin Bafut, kusa da Bamenda, a yankin Arewa maso yammacin kasar ranar litinin da ake komawa karatu daga hutu.

Ko a baya fursunoni 160 ne suka tsere daga wani gidan yari da ke yankin Arewa maso yammacin kasar.

Bayanai sun ce ‘yan bindiga kusan 50 ne suka afka wa gidan yarin tare bude wuta akan jami’an tsaro, inda daga bisani su ka balle kofofin gidan yarin.

Wani jami’in gwamnatin lardin da lamarin ya faru William Emvouto Bbita, ya ce bayan balle kofofin gidan yarin, maharan sun banka wa baki dayan gidan yarin wuta.

Rikicin yan aware a Kamaru yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama, da kuma raba sama da 200,000 da muhallin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI