Afrika ta Kudu

Tattalin arzikin Afrika ta kudu ya samu koma baya

Cyril Ramaphosa Shugaban Afrika ta kudu
Cyril Ramaphosa Shugaban Afrika ta kudu Themba Hadebe / POOL / AFP

Kasar Afirka ta kudu, kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a Afirka bayan Najeriya, ta samu koma bayan tattalin arzikin ta, kamar yadda alakaluma suka nuna cewar rahotan watanni 3 tsakanin Afrilu zuwa Yunin wannan shekara tattalin arzikin kasar ya samun koma bayan kasa da maki guda.

Talla

Bayanai sun ce an samu koma bayan ne a bangaren noma da sufuri da kasuwanci da kuma bangaren masana’antu.

Wannan dai ba karamar koma baya bane ga shugaba Cyril Ramaphosa, wanda ya sha alwashin bunkasa tattain arzikin kasar bayan maye gurbin shugaba Jacob Zuma.

15 ga watan Fabrairu 2018 ne Majalisar Dokokin Afrika ta Kudu ta zabi Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugaban kasar bayan Jacob Zuma ya yi murabus sakamakon matsin lambar da ya sha daga jam’iyyrsa ta ANC saboda zargin cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI