Afrika ta Kudu

Fararen fata fiye da dubu 2 na zanga zanga yau a Afrika ta kudu

Matakin dai na zuwa ne bisa wani yunkurin gwamnatin Afrika ta kudun kan samar da daidaiton mallakin kadarori tsakanin bakaken fata da fararen fatar kasar.
Matakin dai na zuwa ne bisa wani yunkurin gwamnatin Afrika ta kudun kan samar da daidaiton mallakin kadarori tsakanin bakaken fata da fararen fatar kasar. REUTERS/Zoubeir Souissi

Akalla fararen fata 2,000 yau suka shiga wata zanga zanga a Afirka ta kudu domin nuna rashin amincewar su da yunkurin wani kamfani hada magunguna na Sasol kan bai wa ma’aikatan sa bakaken fata hannun jari a cikin sa.

Talla

Jagoran masu zanga zangar Dirk Hermann ya ce ba za su amince da shirin sake fasalin kamfanin na kaucewa wariyar da aka yi wa bakaken fata a baya ba, da kuma yi wa fararen fata wariya yanzu.

Hermann ya ce bai wa bakaken fata zalla hannun jarin yanzu zai tada ciwon da aka samu baya, lokacin da ake nuna musu wariya.

Shi dai kamfanin ya bayyana shirin bai wa bakaken fatar 6,300 wani kaso na hannun jarin ne domin sauya yadda ake tafiyar da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.