Sudan ta Kudu

Kotun Sudan ta kudu ta hukunta sojin da suka kashe dan jarida

Alkalin ya wanke soja guda da ake zargi, yayin da yace wani kwamandan sojin da aka zarga da sa ido lokacin aikata laifin ya mutu a gidan yari bara.
Alkalin ya wanke soja guda da ake zargi, yayin da yace wani kwamandan sojin da aka zarga da sa ido lokacin aikata laifin ya mutu a gidan yari bara. REUTERS

Wata Kotu a Sudan ta kudu ta yanke hukuncin daurin shekaru 7 ga wasu sojojin kasar guda 10 da aka samu da kashe wani dan jarida da kuma yi wa jami’an agajin kasashen duniya 5 fyade.

Talla

Mai shari’a Knight Baryano Almas, wanda ya dauki dogon lokaci ya na bayani kan zargin fyaden da kashe dan jarida da sata da kuma lalata dukiya da ake yi wa sojojin, ya ce kotun sojin ta tabbatar da laifin akan su, sakamakon shaidun da aka gabatar mata.

Alkalin ya wanke soja guda da ake zargi, yayinda ya ce wani kwamandan sojin da aka zarga da sa ido lokacin aikata laifin yamutu a gidan yari bara.

Hukuncin da alkalin ya bayyana ya sanar da daure sojoji 2 rai da rai saboda kashe dan jaridar John Gatluak da kuma aikata fyade da wasu kaifufuka na dabam, yayin da sauran kuma aka yanke musu hukuncin daurin tsakanin shekaru 7 zuwa 14.

An dai samu tashin hankalin ne a watan Yulin shekarar 2016 a Juba, lokacin da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakin sa Riek Machar ta warware.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI