Burkina-Faso

sojojin Burkina Faso biyu sun mutu, wasu shida sun jikkata a wani harin ta'adanci

sojojin dake yaki da yan ta'ada a kasar Mali
sojojin dake yaki da yan ta'ada a kasar Mali ©Daphné BENOIT / AFP

Sojojin Burkina Faso biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 6 suka samu raunuka bayan da motar da suke tafiya a ciki ta taka nakiyar da aka binne a gefen hanya.Lamarin ya faru ne a kusa da wani gari da ake kira Kabonga da ke gabashin kasar kusa da iyaka da Mali, yankin da ya sha fuskantar hare-haren ‘yan bindiga masu nasaba tsatsauran ra’ayin addini.

Talla

Wata majiyar tsaro ta bayyana sojojin da zama masu aikin warware nakiya da aka aika a yankin domin warware wata nakiyar gargajiya da ake zargin yan ta’addar na amfani da ita wajen kai hare harensu a yankin

Idan dai ba a mata ba a makon da ya gabata sojojin kasar ta Burkina Faso 7 suka rasa rayukansu a cikin wata fashewar nakiyar gargajiya, makwanni 2 baya mutuwar wasu mutane 6, duk a cikin yanayi makamncin na farko a yankin dake gabashin kasar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.