Bakonmu a Yau

Farfesa Abba Abubakar Haladu kan ranar yaki da Jahilci a duniya da hukumar UNESCO ta ware

Wallafawa ranar:

Hukumar Kula da ilimi, al’adu da kimiyya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowacce ranar 8 ga watan Satumba a matsayin ranar yaki da jahilci, inda ake nazarin kokarin da ake na tabbatar da cewar kowanne Bil Adama ya samu ilimi.

Najeriya na daga cikinn jerin kasashen da ake fama da marasa ilimi a duniya a cewar hukumar yaki da jahilci ta kasar.
Najeriya na daga cikinn jerin kasashen da ake fama da marasa ilimi a duniya a cewar hukumar yaki da jahilci ta kasar. UNHCR/K.Mahoney
Talla

Wannan ya sa yau ake gudanar da bukukuwa a birnin Paris domin tattauna cigaban da aka samu da wadanda suka bada gudumawa wajen samar da ilimi da kuma koyawa jama’a sana’oi domin karrama su.

Najeriya na daya daga cikin kasashen dake da yawan marasa ilimin, kamar yadda shugaban hukumar yaki da jahilci Farfesa Abba Abubakar Haladu yace adadin su ya kai sama da miliyan 60.

Muhammad Sani Abubakar ya tattauna da Farfesa Haladu akan aikin samar da ilimin, kuma ga yadda hirar su ta gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi