Najeriya-Shia

Mabiya Shi'a sun yi zanga-zangar cikar Zakzaky kwana dubu a tsare

Dubun dubatar mabiya shi’a ne yau suka gudanar da wata zanga-zanga a Abuja babbar birnin Najeriya don nuna adawa da ci gaba da tsare jagoransu Ibrahim Yakubu Zakzaky wanda yanzu haka ke cika kwanaki dubu daya a hannun gwamnatin kasar.

Wasu jiga-jigan mabiya Shi'a kenan yayin zanga-zangar Lumana da suka gudanar yau Juma'a a Abuja don nuna alhininsu da cikar Jagoransu Ibrahim Zakzaky kwanaki dubu daya a hannun gwamnatin Najeriya.
Wasu jiga-jigan mabiya Shi'a kenan yayin zanga-zangar Lumana da suka gudanar yau Juma'a a Abuja don nuna alhininsu da cikar Jagoransu Ibrahim Zakzaky kwanaki dubu daya a hannun gwamnatin Najeriya. rfihausa
Talla

Mabiyan sun faro zanga-zangar ta yau ne tun daga kasuwar Wuse da ke tsakiyar babban birnin Najeriyar har zuwa Sakatariyar gwamnatin kasar, ba kuma tare da wata hatsaniya ba.

A baya dai matukar mabiyan za su gudanar da makamanciyar zanga-zangar ta kan juye zuwa rikici tsakaninsu da jami’an tsaron kasar da zai kai ga lalata dukiyoyin jama’a a wasu lokutan ma har da rasa rayuka.

Tun a watan Disamban 2015 ne gwamnatin Najeriyar ke tsare da Zakzaky bayan wani artabu tsakanin mabiyanshi da dakarun sojin kasar da ya kai ga rasa rayuka.

Lamarin dai faro ne tun daga lokacin da mabiyan na Shi’a suka rufe hanya tare da hana Babban hafson sojin Najeriya Tukur Burutai wucewa baya ga kisan soji guda.

Gwamnatin na Tuhumar Zakzaky da matarsa tare da wasu mutane biyu da tarin laifuka ciki har da hada baki wajen aikata kisan jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI