Najeriya

Ganawar manyan jami'an APC da tsohon gwamnan Kano Shekarau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole Duisaf.com

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Adams Oshiomhole, ya ce ganawarsu jiya juma’a da tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekaru wanda jigo ne a jam’iyyar PDP mai adawa ta yi armashi.

Talla

Oshiomhole wanda ke tare da rakiyar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma wasu kusoshin jam’iyyar APC, sun gana da Shekarau ne a birnin Kano kwanaki kadan bayan da wani na hannun damansa ya ce tsohon gwamnan ya canza sheka daga PDP zuwa APC, labarin da daga bisani ya musanta da kansa.

Wasu majiyoyi sun ce a lokacin ganawar, jam’iyyar APC ta yi wa tsohon gwamna Shekarau alkawarin ba shi tikitin tsayawa takarar kujerar dan majalisar dattawa da ke wakiltar Kano ta tsakiya, wadda ita ce mazabar tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da wasu bayanai ke cewa abu ne mai yiyuwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa makusanta Shekarau mukamai a cikin gwamnatinsa nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.