Senegal

Senegal za ta dauki nauyin wasannin Olympics na matasa a 2022

Bikin bude wasannin Olympics a Koriya
Bikin bude wasannin Olympics a Koriya REUTERS/John Sibley

Kwamitin shirya wasannin Olympics a duniya ya amince Senegal ta daukin shirya wasannin Olympics ajin matasa karo na 4 da za a yi shekara ta 2022 idan Allah ya kai mu.

Talla

A cikin watan oktoba mai zuwa ne taron koli na kwamitin Olympics da za a yi a birnin Buenos Aires na kasar Argentina zai tabbatar wa Senegal wannan dama a hukumance.

Senegal dai ta yi takarar samun wannan dama ce da kasashen Afirka uku da suka hada da Tunisia, Botswana da kuma Najeriya.

Wannan zai kasance karo na farko da wata kasa ta Afirrka za ta dauki nauyin shirya irin wadannan wasanni a tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI