Najeriya

Shekarau ya tabbatar da komawarsa APC daga PDP

Tsohon Gwamnan jihar Kano da ke Arewacin Najeriya kuma tsohon dan takarar shugabancin kasar Malam Ibrahim Shekarau.
Tsohon Gwamnan jihar Kano da ke Arewacin Najeriya kuma tsohon dan takarar shugabancin kasar Malam Ibrahim Shekarau. Solacebase

Tsohon gwamnan jihar kano Ibrahim Shekarau wanda ke matsayin jigo a Jam’iyyar adawa ta Najeriya PDP ya sanar da kammala komawarsa jam’iyyar APC mai mulkin kasar yau Asabar.

Talla

Ibrahim Shekarau wanda ya tsaya neman kujerar shugabancin Najeriya a 2011 ya sanar da komawar ta sa APC ne a hukumance yau Asabar yayin wani taro dfa ya yi da magoya bayansa a gidansa da ke Mundubawa a jihar ta Kano.

A cewarsa ya sauya shekar ne sakamakon rashin adalcin da ya ke fuskanta a PDP musamman kan abin da ya shafi shugabancin jiha wanda ya mayar da shi da magoya bayansa saniyar ware.

Sai dai yayin ayyana komawar APC na Shekarau ba a ga wasu daga cikin jiga-jigan magoya bayansa da suka kunshi Salihu Sagir Takai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.