Najeriya

Zaben Najeriya: Sarkin Musulmi ya ja hankalun shugabannin addinai

Mai Alfarma Saerkin Musulmin Najeriya Sa'ad Abubakar na Uku
Mai Alfarma Saerkin Musulmin Najeriya Sa'ad Abubakar na Uku rfi-Hausa

Mai alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci shugabannin addinai da su ja hankulan mabiyansu domin kaucewa tashin hankali musamman ma a daidai lokacin da kasar ke shirye-shiryen gudanar da zabubuka.

Talla

Sarkin Musulmi na wannan kira ne a lokacin da yake ganawa da tawagar manyan limaman cocin Katolika da suka ziyarce shi a birnin Sokoto ranar juma’a.

Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce ‘lokaci ya yi da ya kamata a gaya wa juna gaskiya a Najeriya, domin kuwa akwai abubuwan da ba sa tafiya daidai a kasar, sakamakon yadda jama’a ke fakewa da addini ko kabilanci domin biyan bukatunsu musamman a irin wannan yanayi na siyasa’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI