Burkina-Faso

Burkina Faso za ta kaddamar da sabon yaki kan 'yan ta'adda

Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré, ranar 28 ga watan nuwambar 2017.
Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré, ranar 28 ga watan nuwambar 2017. LUDOVIC MARIN / POOL / AFP

Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, ya bai wa dakarun kasar umarnin kaddamar da farmaki a yankin gabashi da kuma kudu maso yammacin kasar iyaka da Mali domin kawo karshen kutsen ‘yan bindiga da kan yi sanadiyyar mutuwar mutune da dama a kasar.

Talla

Kabore wanda ya jaogranci taron gaggawa jiya asabar kan sha’anin tsaro jim kadan bayan dawowarsa daga taron kasashen Afirka da China, ya ce Burkina Faso za ta dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin kare rayukan jama’a da kuma dukiyoyinsu a wadannan yankuna, bayan share tsawon watanni ana samu hare-hare daga ‘yan bindiga da aka bayyana cewa suna shiga kasar ne daga Mali.

Yanzu haka dai ma’aikatan gwamnati ciki har da malaman makarantu na cigaba da tserewa daga wadannan yankuna, domin kaucewa barazanar da suke fuskanta daga ‘yan bindigar.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI