Libya-'Yan cirani

Fatake na yaudarar 'yan ci-rani a Libya

Bakin hauren da suka makale a Libya a hanyarsu ta zuwa Turai
Bakin hauren da suka makale a Libya a hanyarsu ta zuwa Turai REUTERS/Hani Amara

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta ce tabbas, wasu fatake na amfani da suna ko kuma alamunta domin yin safarar ‘yan cirani daga kasar Libya zuwa yankin Turai.

Talla

Mai magana da yawun hukumar ta UNHCR a birnin Geneva Bara Baloch, ya ce tuni suka kaddamar da bincike bayan kama wasu mutane sanye da tufafin jami’an hukumar a daidai lokacin da suke safarar bakin zuwa ketare.

To sai dai ya ce duk wani yunkuri da MDD za ta yi domin shawo kan wannan matsala ba zai taba samu nasara ba sai tare da hadin gwiwar mahukuntan kasar Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI