Mauritania

Jam'iyya mai mulki na gaf da lashe zaben kasar Mauritania

Wata mata na kada kuri'a a zaben 'yan Majalisar Mauritania, ranar 1 ga watan satumbar 2018
Wata mata na kada kuri'a a zaben 'yan Majalisar Mauritania, ranar 1 ga watan satumbar 2018 AHMED OULD MOHAMED OULD ELHADJ / AFP

Jam’iyyar UPR mai mulki a Mauritania ta lashe kujeru 67 daga cikin 157 a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da aka yi a makon jiya, yayin da ‘yan adawa suka tashi da kujeru 31 kamar yadda sakamakon zaben ya nuna.

Talla

Ita ma jam’iyyar Tawassoul ta masu ra’ayin addinin Islama ta samu kujeru 14.

To sai dai za a gudanar da zagaye na biyu na zaben domin cike gurbin sauran kujerun majalisar a ranar asabar ta makon gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI