Masar-MDD

MDD ta nemi janye hukuncin kisan mutane 75 a Masar

Babbar jami’ar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta bukaci kotun daukaka karar Masar ta dakatar da hukuncin kisan mutane 75 da ta yanke jiya tare da mika batun ga kananan kotunan kasar don yanke hukuncin.

A cewar Barchelet matukar mahukuntan Masar suka zuba ido aka kashe mutane 75 hukuncin zai zamo mafi munin cin zarafin bil'ada da kotu ta aikata.
A cewar Barchelet matukar mahukuntan Masar suka zuba ido aka kashe mutane 75 hukuncin zai zamo mafi munin cin zarafin bil'ada da kotu ta aikata. Presidencia de Chile
Talla

Bachelet wadda ta ce Kotun bata tasamma adalci ba a hukuncin na ta na jiya wanda ya zartas da hukuncin kisa ga mutanen 75 magoya bayan tsohon shugaban kasar Muhammad Morsi, ya ce hukuncin ya keta hakkin bil’adama

Hukuncin kotun na jiya dai ya zargi mutanen 75 da haddasa rikicin da ya kai ga kisan daruruwan jami’an tsaron kasar yayin wani bore da ya juye zuwa rikici a sassan na Masar cikin shekarar 2011.

Sai dai babbar jami’ar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce matukar hukumomin kasar suka zuba ido aka zartas da hukuncin kisan kan mutane 75 babu shakka zai zama mafi munin hukuncin da aka zartas bisa son rai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI