Najeriya

Sojojin Najeriya sun yi ikirarin sake kwato Gudumbali

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da sake kwato garin Gudumbali daga hannun Boko Haram, bayan da mayakan rahotanni suka ce mayakan sun mamaye wanan gari da ke jihar Borno a ranar asabar da ta gabata.

Talla

Kakakin rundunar tsaron Najeriya Burgediya Janar Texas Chukwu, wanda a jiya asabar ya ce ba ya da masaniya game da labarin da ke cewa ‘yan Boko Haram sun kwace garin, a wannan lahadi ya ce ‘’tabbas an yi wani artabu a yankin tare da kona gidaje da dama, amma daga bisani maharan sun janye’’.

Janar Chukwu ya ce ba a samu asarar rayuka ba,  sannan kawo yanzu an dawo da doka da oda tare da tura karin sojoji zuwa yankin’’ a cewarsa.

A ranar asabar da ta gabata ne bayanai suka nuna cewa wani adadi mai tarin yawa na ‘yan Boko Haram ya kwace ikon garin na Gudumbali bayan da suka fatattaki sojojin da ke cikin wani bariki a yankin.

Har ila yau bayanan farko sun ce an kashe fararen hula akalla 8 lokacin wannan artabu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI