Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Mahara sun kashe mutane 9 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Sojojin Minusca a birnin Bangui.
Sojojin Minusca a birnin Bangui. AFP PHOTO/PACOME PABANDJI

An gano gawarwakin mutane 9 wadanda ‘yan bindiga suka yi awun gaba da su daga wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Bria a Jamhuriyar Afrika ta Afirka.

Talla

Mai magana da yawun rundunar MDD a kasar Vladimir Monteiro, ya bukaci jama’a su kwantar da hankula, bayan da wasu ‘yan gundun hijira suka gudanar da zanga-zanga a harabar ginin Majalisar da ke birnin Bangui domin nuna bacin ransu dangane da abin da suka kira sakaci da kuma kin bai wa fararen hula kariya a kasar.

Rahotanni sun ce dakarun wata kungiya mai suna FPRC ne suka kai sace mutanen kafin su kashe su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.