Najeriya

'Yan Boko Haram sun kwace ikon garin Gudumbali

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a gaban baradensa
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a gaban baradensa © AFP PHOTO / BOKO HARAM

A Najeriya bayanai sun tabbatar da cewa yanzu haka mayakan Boko Haram ne ke cigaba da iko da garin Gudumbali da ke jihar Borno, bayan da suka fatattaki sojoji daga barikinsu da ke yankin.

Talla

Rahotanni sun ce mayakan na Boko Haram sun yi nasarar kwace garin ne tun a ranar asabar da ta gabata, bayan wani mummun farmaki da ya tilasta wa sojoji arcewa daga barikin, lamarin da ya kasance irinsa na farko a cikin shekaru biyu.

Shaidu sun ce an kashe wani adadi na fararen hula a lokacin artabun, inda kungiyoyin agaji ke cewa jama’a dama ne suka tsere sannan kuma suke cikin bukatar samun tallafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI