S. Africa

Ana kashe mutane 57 a kowacce rana a Afrika ta Kudu

Jami'an 'yan sandan Afrika ta Kudu sun ce suna aiki tukuru don dakile kisan-kai a kasar
Jami'an 'yan sandan Afrika ta Kudu sun ce suna aiki tukuru don dakile kisan-kai a kasar Photo: Reuters/Rogan Ward

Alkaluman kisan-kai a Afrika ta Kudu sun karu, in da sabuwar kididdigar da aka fitar a wannan Talatar ke nuna cewa, sama da mutane dubu 20 aka kashe a sasssan kasar a bara kadai, wato kwatankwacin rayuka 57 ke salwanta ta wannan hanyar a kowacce rana.

Talla

Kididdigar ta nuna cewa, kimanin mutane 57 ake kashewa a kowacce rana a Afrika ta Kudu a bara, yayin da rundunar ’yan sandan kasar ta ce, tana aiki tukuru don shawo kan matsalar.

A jumulce dai, mutane dubu 20 da 336 aka kashe a cikin watanni 12, adadin da ya zarce na shekarar 2016 da aka kashe mutane dubu 19 da 16.

Alkaluman na nuna cewa, ana samun karuwar kisan kai da kashi 6.9, kuma wannan adadin na daya daga cikin mafi munin dai-daikun kisan kai da kasar ta gamu da shi tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata shekaru 24 da suka gabata.

Ministan ‘Yan Sandan Kasar, Bheki Cele ya shaida wa manema labarai cewa, duk da wannan adadi na kisan a kowacce rana, akwai zaman lafiya a Afrika ta Kudu mai iyaka da kasashen da ke fama da rikici.

Sai dai jami’in ya ce, matsalar ta kisan-kai na razana shi a koda yaushe.

Jami’in ya kuma bukaci ‘yan kasar da kada su kalli matsalar kai musu hari da kisa a kowacce rana a matsayin wata al’ada domin ya dace su dauki matakin kawo sauyi ga lamarin a cewarsa.

Ana yawan caccakar rundunar ‘yan sandan Afrika ta Kudu saboda gazawarta wajen takaita manyan laifukan da ake tafkawa a kasar, yayin da rundunar ke cewa tana bukatar akalla karin jami’ai dubu 62.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.