Eritrea-Habasha

An bude iyakokin Eritrea da Habasha bayan shekaru 20 a kulle

Kasashen Habasha da Eritrea sun sanar da bude iyakokinsu ta kasa a hukumance karon farko cikin shekaru 20, matakin da ke nuna ci gaba da daidaituwar alaka tsakaninsu a baya-bayan nan.

Firaminista Abiy Ahmed da takwaransa Isaias Afwerki yayin sanya hannu kan wata sanarwa da ke kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu ranar 9 ga watan Yulin 2018.
Firaminista Abiy Ahmed da takwaransa Isaias Afwerki yayin sanya hannu kan wata sanarwa da ke kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu ranar 9 ga watan Yulin 2018. Twitter/Yemane G. Meskel
Talla

Ma'aikatar yada labaran Eritrea ta ce Firaminista Abiy Ahmed da kansa ya halarci taron bude kan iyakokin bayan kasancewarsu a rufe tsawon shekaru sakamakon tsamin alakar da ke tsakaninsu.

Iyakokin da aka gudanar da bikin budewar ta su sun hadar da na Gabashin kasar da na yammaci wadanda aka kullesu a shekarar 1998 bayan yanke huldar Diflomasiyya tsakanin kasashen na Eritrea da Habasha sakamakon yakin shekaru 2 da suka shafe suna tafkawa.

Bude iyakokin na daga cikin matakan baya bayan nan da shugabannin kasashen biyu ke dauka wajen ganin sun kawo karshen rashin fahimtar da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI