Bakonmu a Yau

Farfesa Garba Danbatta kan inganta harkar sadarwa

Sauti 04:01
Masana na daukan matakan inganta harkar sadarwa a duniya
Masana na daukan matakan inganta harkar sadarwa a duniya (Photo : ESA)

Masu ruwa da tsaki kan harkar sadarwa a duniya na halartar wani taro da ke a Durban da ke Afrika ta Kudu, in da ake gabatar da ci gaban fasahar da aka samu a fannin, tattauna matsaloli da kuma sabbin dabarun inganta harkar sadarwar da kuma zuba jari. Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke halartar taron, kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban Hukumar Sadarwar Kasar, Farfesa Umar Garba Danbatta.