Faransa-Aljeriya

Faransa ta amsa laifin azabtar da 'yan Algeria a yakin kasar na 1954

A cewar Macron shi ne ya cancanci ya nemi yafiyar mai dakin ta Audin bisa kisan mai gidanta haka zalika baya bukatar godiya daga gareta.
A cewar Macron shi ne ya cancanci ya nemi yafiyar mai dakin ta Audin bisa kisan mai gidanta haka zalika baya bukatar godiya daga gareta. LUDOVIC MARIN/ AFP

Gwamnatin Faransa ta amsa zargin cewa ta yi amfani da wasu tsare-tsare da suka kai ga azabtar da tarin jama’a a Algeria, yayin fafutukar neman ‘yancin da kasar ta yi a tsakanin shekaru 1954 zuwa 1962.

Talla

Shugaba Emmanuel Macron wanda aka haifa shekaru da dama bayan fafutukar al’ummar kasar ta Algeria wajen neman ‘yancinsu daga Faransa, shi ne shugaban kasar na farko da ya amsa cewa dakarun sojinsu sun ci zarafi tare da keta haddin dubun-dubatar ‘yan kasar ta Algeria.

A wasu bayanai da ya gabatar, Macron ya tabbatar da cewa sojin Faransa ne suka azabtar tare da hallaka fitaccen masanin lissafi nan na Algerian Maurice Audin wanda aka nema aka rasa tsakanin shekarar 1957, bayan fafutukarsa ta neman ‘yancin daga Faransa.

A ziyarar Macron ga Uwargidan Audin, Josette Audin ya sha alwashin bude rumbun adana bayanan fararen hula dama sojojin da suka bace yayin rikicin na Algeria da ya kunshi ‘yan kasar da kuma Faransawa.

A cewar Macron shi ne ya cancanci ya nemi yafiyar mai dakin ta Audin bisa kisan mai gidanta haka zalika baya bukatar godiya daga gareta.

Wata sanarwar fadar gwamnatin ta Faransa ta ce damar da aka bai wa jami’an soji na wanzar da zaman lafiya a kasar ta Algeria yayin boren neman ‘yancin da ya juye zuwa yaki, shi ne ya bude kofar azabtarwa da suka yiwa fararen hula a bangarori daban-daban.

Yayin kazamin yakin na Algeria an yi ittifakin sojin Faransa sun hallaka al’ummar kasar fiye da miliyan daya da rabi wanda kuma shi ne ya kawo karshen mulkin mallakar tsawon shekaru 130.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI