Afrika-lafiya

An yiwa Mata miliyan 55 Kaciya a kasashe 3 na Afrika -rahoto

Rahotan ya ce kasashe irin su Chadi da Liberia da Mali da Saliyo da Somalia da kuma Sudan da ke dauke da ‘Yam mata miliyan 16 sun ki haramta yin kaciyar.
Rahotan ya ce kasashe irin su Chadi da Liberia da Mali da Saliyo da Somalia da kuma Sudan da ke dauke da ‘Yam mata miliyan 16 sun ki haramta yin kaciyar. Reuters/James Akena

Masu yaki da yi wa mata kaciya a duniya, sun bayyana cewar yanzu haka miliyoyin ‘Yam mata a nahiyar Afirka na fuskantar barazanar yi musu kaciya saboda gazawar gwamnatocin kasashen su na aiwatar da dokokin da suka hana haka.Rahotan ya ce kasashe irin su Chadi da Liberia da Mali da Saliyo da Somalia da kuma Sudan da ke dauke da ‘Yam mata miliyan 16 sun ki haramta yin kaciyar.

Talla

Binciken da wasu lauyoyi 125 daga kasashen duniya suka gudanar kan kasashe 28 inda kaciyar ta zama jiki, ya nuna cewar wadanan kasashe sun gaza kare lafiyar wadannan yara daga fuskantar wannan bala’i da ke jefa rayuwar cikin tashin hankali.

Shugabannin kasashen duniya sun yi alkawari kauda matsalar wadda ta kunshi cire wani sashe na al’aurar mace wanda ya shafi ‘Yam mata da mata sama da miliyan 200, a karkashin yarjejeniyar da suka kulla a shekarar 2015, amma dokokin da aka amince da su a kasashe 22 da suka haramta al’adar sun gaza, saboda karancin masu gabatar da kara da kuma hukunci mai tsanani.

Ann Marie Wilson, Babbar Daraktar kungiyar da ke yaki da al’adar da ake kira ‘28 Too Many’ ta ce akwai gibi sosai wajen dakile al’adar saboda rashin karfin doka.

Rahotan ya ce al’ummomi da dama da ke amfani da al’adar na kallon ta a matsayin wadda ke daga darajar mace da kuma inganta auran ta.

Wadanda suka rubuta rahotan suka ce akalla Yam mata miliyan 55 da ke kasa da shekaru 15 aka yi wa kaciyar, kuma rabin su na zama ne a Masar da Habasha da kuma Najeriya.

Rahotan ya ce Kenya da Uganda ne kawai suka sanya doka mai karfi na yaki da dabi’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.