Jamhuriyar Congo

Congo ta yi barazanar ficewa daga kotun duniya

Jean-Pierre Bemba agaban kotun duniya CPI, le 21 yuni 2016.
Jean-Pierre Bemba agaban kotun duniya CPI, le 21 yuni 2016. REUTERS/Michael Kooren/

Kasar jamhuriyar demkradiyar congo ta yi barazanar ficewa daga kotun duniya (ICC), kwanaki biyu da daukaka karar wani hukumci da aka zartar dan dan adawar kasar ta Congo Jean-Pierre Bemba, da hukumar zaben kasar ta kora daga takarar shugabancn kasar da za a yi a ranar 23 ga watan desember da ya gabata.

Talla

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harakokin wajen kasar ta Congo ta fitar ta ce kasar bata cire tsammanin ficewa daga zama mambar kotun ba, sakamakon abinda ta kira ta gano wasu kasashe na yi wa alkalan kotun matsin lamba, kan al’amarin dake da alkalan da zaben kasar da za a guidanar a ranar 23 ga watan Desembar wannan shekara

A cikin sanarwar gwamnatin ta kongo, ta bayyana shakunta kan wanke M. Bemba da kotun ta duniya ta yi a ranar litanin da ta gabata, wanda ya sake bashi damar komawa a kara da shi a zaben shugabancin kasar.

Duk an zaci, kotun ta CPI ta tuhumi tsohon shugaban yan tawayen, kan laifin gabatar da shaidun karya a shara’arsa da ta hada shi da ita ta aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a kasar jamhuriya Afrika ta tsakkiya.

A matsayin sa na babban abokin hamayar shugaba Joseph Kabila, kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar ta Congo, ta haramtawa M. Bemba tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar, sakamakon tuhumar da ta yi masa da farko na gabatar da shaidun na karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.