Chadi

Sojan Chadi sun kashe fararen hula biyu

Shugaba Idriss Deby yana bayani ga manema labarai wani lokaci da dadewa
Shugaba Idriss Deby yana bayani ga manema labarai wani lokaci da dadewa REUTERS

Wani jirgin saman sojan kasar Chadi mai saukan ungulu ya kashe wasu fararen hula biyu dake hakar ma'adinai a wani gari dake kan iyakan Chadi da Libya, daidai inda Dakarun Chadi ke fafatawa da kungiyoyin ‘yan tawaye.

Talla

Ganau sun bayyana cewa jiragen yakin Chadi masu saukan ungulu su biyu suka rika kai hare-hare a garin Kouri Bougoudi inda suka kashe mutanen biyu.

Wasu fararen hulan biyu kuma na chan da raunuka

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.