Uganda

Ana zargin kungiyar Lords Resistance Army da cin zarafin jama’a

Lauyan dake kare shugaban yan Tawayen Uganda a kotun hukunta manyan laifuffuka ya bukaci sakin Dominic Ongwen da yake karewa, inda yake cewa kungiyar yan tawayen Lords Resistance Army taci zarafin sa lokacin yana karami.

Joseph Kony, Shugaban kungiyar yan tawaye ta LRA a Uganda
Joseph Kony, Shugaban kungiyar yan tawaye ta LRA a Uganda Reuters/Stuart Price/Pool
Talla

Lauya Krispus Ayena Odongo yace wanda yake karewa ya fuskancin azabtarwa daga kungiyar LRA dake karkashin Joseph Kony, mutumin da ake nema ruwa ajallo.

Dominic Ongwen na fuskantar zarge zarge 70 da suka hada da ayyukan ta’addanci.

Majalisar Dinkin Duniya na zargin kungiyar LRA da kashe mutane sama da 10,000 da kuma sace yara 60,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI