Bakonmu a Yau

Annobar amai da gudawa ta yi mummunan ta'adi a yankin Tafkin Chadi

Wallafawa ranar:

Hukumar kula da ayyukan jinkai ta MDD ta ce akalla mutane 510 ne suka rasa rayukansu sakamakon annobar amai da gudawa a kasashen da ke zagaye da tafkin Chadi.Alkalumman da hukumar ta OCHA ta tattara, na nuni da cewa saama da mutane dubu 27 ne suka kamu da wannan cuta a yankin da ya hada kasashen Chad, Nigeria, Kamaru da kuma Nijar.Dakta Abdullahi Isah Kauran Mata, kwararren likita ne a asibitin koyarwa ta Malam Aminu Kano, ga abin da yake cewa dangane da wadannan alkaluma a zantawarsu da Abdulkarim Ibrahim Shikal.

Cibiyar kula da masu fama da cutar amai da gudawa ta MSF, a Jamhuriyar Congo
Cibiyar kula da masu fama da cutar amai da gudawa ta MSF, a Jamhuriyar Congo LIONEL HEALING / AFP
Sauran kashi-kashi