Tanzania

Shugaban Tanzaniya ya bada umarnin kama masu kwale-kwale da yakashe daruruwan mutane

Shugaban kasar Tanzania John Magafuli ya umurci da a kama mahukuntan kamfanin zirga zirgan kwale kwalen nan da ya kife a Tafkin Victoria, yayinda yawan mutanen da suka mutu ya zarta 136.Ana zaton kwale kwalen na dauke da fiye da fasinjoji 200 ne, adadin da ya ninka iya mutanen da ya kamata ya diba, lamarin da ya sa ya kife a tsibirin Ukrah.

Gabar Tafkin Victoria, in da aka yi hatsarin kwale-kwale
Gabar Tafkin Victoria, in da aka yi hatsarin kwale-kwale sarahemcc/Wikimedia Commons
Talla

Kimanin mutane 136 aka tabbatar da mutuwarsu yayin da aka ceto 102 daga cikin sama da fasinjoji 400 da ke cikin kwale-kwalen.

Tuni al’ummar yankin suka shiga aikin taimako tare da jami’an bada agajin gaggawa don ceto wadanda ibtila’in ya rutsa da su a ranar Alhamis.

Gwamnatin Tanzania ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ba ta yi karin haske ba kan adadin mutanen da ke cikin kwale-kwalen.

Ko a shekarar 1996, sai da sama da mutane 800 suka rasa rayukansu bayan kwale-kwalen da ke dauke da su samfurin MV Bukoba ya yi hatsari a Tanzania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI