Najeriya

Najeriya ta jinkirta kaddamar da sabon kamfanin jiragen sama

Najerya ta jinkirta kaddamar da sabon kamfanin zirga-zirgar jiragen samanta, watanni biyu bayan da kasar ta sanar da wannan shiri.

Tambarin sabon kamfanin jigilar jiragen saman Najeriya
Tambarin sabon kamfanin jigilar jiragen saman Najeriya Ministry of Aviation-Nigeria
Talla

Minista a ma’aikatar kula da zirga-zirgar jiragen sama a kasar, Hadi Sirika wanda ya sanar a cikin watan Yulin da ya gabata cewa, gwamnati za ta kaddamar da kamfani mai suna Nigeria Air, shi da kansa ne ya sanar da jinkirin a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tweeter.

A cikin sanarwar ministan ya bayyana cewa "Ina mai nadamar sanar da ku cewa Majalisar Koli ta Tarayyar ta dauki matakin dakatar da shirin samar da kamfanin jiragen sama na kasa.’’

Minista Sirika bai bayyana dalilan daukar wannan mataki ba, to sai dai manazarta na danganta hakan da irin makuddan kudaden da ake bukata domin aiwatar da shi.

Najeriya, kasar da ta fi kowace yawan jama’a a Afirka, kamfanin jiragenta mai suna Nigeria Airways ya ruguje tun a shekara ta 2003 sakamakon dimbin basusuka, yayin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi alkawarin kafa wani sabon kamfani domin maye gurbinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI