Kamaru

Paul Biya ya mamaye kafafen yada labaran Kamaru-'Yan adawa

Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya © AFP PHOTO / REINNIER KAZE

Wasu ‘yan takarar shugabancin kasar Kamaru su 5, sun zargi kafofin sadarwar gwamnati da fifita yakin neman zaben shugaban kasar mai ci Paul Biya wanda ya sake tsayawa takarar neman shugabanci karo na 6 a zaben da za a yi  ranar 7 ga watan Okotoba mai zuwa.

Talla

‘Yan takarar sun nuna matukar rashin jin dadinsu kan abin da suka kira rashin adalci da kafofin yada labaran na gwamnati ke nunawa a tsakanin ‘yan takarar neman kujerar shugabancin kasar, inda suka bukaci sake komawa bisa tsarin adalci kamar yadda wata sanarwa da suka fitar a ranar laraba ta nuna.

Wadanda suka rattaba wa sanrwar korafin hannu sun hada da babbar jam’iyar adawa ta SDF wadda ta tsayar da Joshua Osih, sai MRC ta dan adawa Maurice Kamto, da  Parti Now! Ta lauayan nan Akere Muna, da kuma gungunan da ke goyon bayan Cabral Libii da Serge Espoir Matomba,  ‘yan takara biyu matasa da za a kara da su a zaben shugabancin kasar ta Kamaru.

‘Yan takarar sun bayyana cewa daukacin lokutan yada labarai a kafafen yada labaran gwamnatin kasar ta Kamaru Talabijin da Radio (CRTV), sun zama  wani dadalin yakin neman zabe da kuma bambadanci ga makusantan jam’iyyar -RDPC", mai mulkin kasar.

Har ila yau ‘yan adawar sun bayyana cewa daga cikin gungun ‘yan rahoto 13 da ke bin ‘yan takarar, 5 an ta’allaka su ne ga Paul Biya da kuma gungun yakin neman zabensa ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.