Tanzania

Mutane 209 ne suka mutu bayan jirkicewar jirgin ruwa a Tanzania

Jirgin ruwan da ya jirkice dauke da fasinjoji a Tanzania
Jirgin ruwan da ya jirkice dauke da fasinjoji a Tanzania Reuters TV/via REUTERS

Rahotanni daga kasar Tanzania na nuni cewa adadin mutane da suka rasa rayukan su hadarin jirgin ruwa da ya kife a tafkin Victoria, daya daga cikin manyan tafkunan Afrika dake kudancin kasar ya karu,Ministan sufurin kasar Isack Kamwelwe da kan sa ne ya bayar da sakamako dake nuni cewa mutane 209 ne suka mutu.

Talla

Shugaban kasar John Magufuli ya ayana zaman makoki na kwanuki hudu tareda bayar da umurni ga jami’an tsaro na su kama duk wanda ke da hannu a wannan hadari.

Binciken farko na nuni cewa jirgin na dauke da yawan jama’a ne ,yayinda wasu rahotani daga mutanen da suka cira da ran su suka bayyana cewa matukin jirgin ya maida hankalin sa zuwa wayar sadarwa dake hannun sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.