Tanzania

Sama da mutane 150 sun hallaka a hadarin jirgin ruwan Tanzania

Jami'an agaji a Tanzania, yayin aikin ciro gawarwakin mutanen da jirginsu ya jirkice a tafkin Victoria.
Jami'an agaji a Tanzania, yayin aikin ciro gawarwakin mutanen da jirginsu ya jirkice a tafkin Victoria. REUTERS/Stringer

Jami'an agaji a Tanzania sun ce yawan wadanda suka hallaka a hadarin jirgin ruwan da ya kife a tafkin Victoria ya karu zuwa mutane 151, daga 136, inda kuma jami’an ke cigaba da neman gawarwakin wadanda ake kyautata zaton sun nutse a tafkin.

Talla

Kafin wannan lokacin dai tuni shugaban Tanzania John Magufuli ya bada umarnin kama wadanda ke kula da jirgin ruwan da yayi hadarin  , ranar alhamis da ta gabata, lamarin da yayi sanadin rasa rayukan fasinjoji masu yawa.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, jirgin ya jirkice ne, sakamakon yadda daruruwan fasinjojin da ke cikinsa suka karkata zuwa barin jirgin guda da nufin shirin sauka, a lokacin da suka kusa isa gabar tafkin na Victoria.

Mafi munin hadarin jirgin ruwan da kasar Tanzania ta taba fuskanta shi ne wanda ya faru a watan Mayu na shekarar 1996, inda kimanin mutane 800 suka hallaka, sakamakon hadarin da jirgin ruwansu yayin da yake kan hanyar zuwa garin Mwanza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI