Sudan ta Kudu

Likitan da ke kula da lafiyar 'yan gudun hijira dubu 144

Dr. Evan Atar Adaha a dakin tiyata mai fitila daya tal
Dr. Evan Atar Adaha a dakin tiyata mai fitila daya tal iafrica.com

Wani likitan Sudan ta Kudu da ke gudanar da wani asibiti mai dauke da tarin marasa lafiya, ya lashe kyautar Majalisar Dinkin Duniya ta shekara kan rawar da yake takawa wajen kula da lafiyar jama’a da suka hada da 'yan gudun hijira sama da dubu 100.

Talla

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta bayyana likitan Dr. Evan Atar Adaha da ke kula da asibitin Maban a garin Bunj a matsayin wanda ke kula da lafiyar 'yan gudun hijira akalla dubu 144 a Jihar Blue Nile dake kan iayaka da kasar Sudan.

Asibitin na da na'urar daukar hoton sassan jikin mara lafiya amma ta lalace, sai dai duk da haka likitan kan yi wa marasa lafiya akalla 60 aikin tiyata a kowanne mako a dakin da ke da fitila guda.

Shugaban Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira Filippo Grande ya ce,  tausayawar Atar ta yi sanadiyar kare lafiyar dubban mutane.

A bara dai, Zannah Mustapha ne ya lashe kyautar daga Najeriya saboda rawar da ya taka wajen ceto daliban makarantar Chibok da Kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a shekarar 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI