Libya

Yara rabin miliyan na fama da yunwa a Libya

Rikicn Libya ya jefa hatta yara cikin matsananciyar yunwa
Rikicn Libya ya jefa hatta yara cikin matsananciyar yunwa AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara rabin miliyan ne ke fama da matsananciyar yunwa a birnin Tripoli na kasar Libya sakamakon yakin  da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin kungiyoyi masu dauke da muggan makamai.

Talla

Hukumar Kula da Ilimin Kananan Yara ta Majaisar Dinkin Duniya, UNICEF ta ce iyalai sama da dubu 1 da 200 sun rasa matsugunansu a cikin sa’oi 48 kadai sakamakon zazzafar fafatawar da ake yi, wanda hakan ya kawo adadin mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa dubu 25 kuma rabinsu, yara ne kanana.

Geert Cappelaere, Daraktan Hukumar UNICEF da ke kula da Arewacin Afrika da Gabas ta Tsakiya ya ce, ana ci gaba da daukar yara kanana ana sanya su cikin aikin soji, abin da ke jefa su cikin hadari, ganin yadda ake kashe yaran lokaci lokaci.

Daraktan ya ce ana amfani da makarantu wajen bai wa mutanen da suka rasa matsugunansu mafaka wanda hakan ya haifar da jinkiri wajen bude makarantun yara, yayin da mazauna yankin ke fama da rashin abinci da ruwan sha da kuma wutar lantarki.

Cappalaere ya ce tashin hankalin ya tilasta wa baki da 'yan gudun hijira cikinsu har da yara kanana barin matsugunansu, yayin da wasu suka fada cikin tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.