Kamaru

Kamfanin jirgin kasa na Kamaru ya yi kisan kai-Kotu

Jirgin kasa na  Camrail da ya kauce hanyarsa a shekarar 2016 tare da kashe mutane 79
Jirgin kasa na Camrail da ya kauce hanyarsa a shekarar 2016 tare da kashe mutane 79 REUTERS/Anne Mireille Nzouankeu

Kotu a kasar kamaru ta samu kamfanin sufurin jiragen kasa na Camrail da shugabanninsa 10 da laifin kisan kai sakamakon hadarin da jirginsu yayi a shekarar 2016 wanda cikinsa mutane 79 suka mutu.

Talla

Daga cikin shugabannin kamfanin sufurin jiragen da aka yanke wa hukunci, akwai tsohon shugabansa Didier Vendenbon.

Sai dai kotun ta wanke wasu mutane uku da aka tsare da fari bisa zargin su da hannu a hadarin jirgin na shekarar 2016 da ya yi sanadin jikkatar mutane 600, baya ga wasu 79 da suka rasa rayukansu.

Wani lokaci nan gaba ake sa ran kotun za ta fayyace irin hukuncin da za ta zartas akan wadanda aka samu da laifin.

A ranar 21 ga watan Okoban 2016, jirgin kasa mallakin kamfanin sufurin jiragen kasar ta kamaru Camrail, ya yi hadari a lokacin da yake kan hanyar zuwa birnin Douala daga Yaounde, in da ya kauce daga kan hanyarsa a gaf da garin Eseka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.